‘Yansandan Najeriya Sun Kama Masu Sace Mutane Tsakanin Kaduna da Abuja

Rundunar 'yansandan Najeriya ta samu nasarar kama wasu gungun masu satar mutane wajen su arba'in kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Masu garkuwa da mutane kimanin su arba’in ne aka kama kan hayar Kaduna zuwa Abuja.

Baicin mutanen , ‘yansandan sun samu cafke bindigogi da kwamfutoci da kayan wuya na mata masu tsada. Sun sami guraye da layu. Haka ma aka sami kayan mutane da suka sace.

Kakakin ‘yansandan Mashud Jimoh yace kwanan nan babban sifetonsu Alhaji Ibrahim Idris ya kaddamar da wani rundunar yaki da masu satar mutane da fashi da makami.

Ko makon jiya ‘yansandan sun cafke muggan mutane fiye da talatin a kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Amma Sabo Imam Gashuwa mai bin hanyar yace lamarin garkuwa da mutane ya dan ragu amma wani dan kasuwa dake Abuja Alhaji Alkali Muhammed yace ‘yansandan wani lokaci suna yin kitso da kwarkwata. Ya bada misalin wani da suke aiki da aka sace sai da suka biya kusan miyan uku kafin a sakoshi.

Asalin Labari:

VOA Hausa

376total visits,1visits today


Karanta:  An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen 'yan sanda

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.