‘Yan Ta’adda sun farwa ofishin EFCC a Abuja

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofishin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Abuja, babban birnin Najeriya.

Yau da safe da misalin karfe 5 na asuba ‘yan ta’adda sun shiga hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC da ke Wuse Zone 7 Abuja.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar sun je wajen ne dauke da bindigogi inda suka fara harbe-harbe a harabar ofishin ‘sun lalata motocin da yawa da suka samu a harabar ofishin  suka kori masu gadin wurin.

Rahotannin sun kara da cewa ‘yan ta’addar sun ajiye wata ambulan, wadda ke dauke da sakon barazana ga shugaban sashen da ke bincike a kan almundahana da ta shafi musayar kudaden waje, Ishaku Sharu.Wannan lamari dai ya faru ne a lokacin da hukumar ke zafafa bincike a kan wadanda ake zargi da almundahana da yin sama da fadi da kudin gwamnati.

Amma masu gadin wurin, sun samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addar. Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya  ce suna iya kokarinsun  don ganin sun fatattake su da wuri kafin su yi barna sosai.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, NAN

475total visits,1visits today


Karanta:  An Daure Wani Ma’aikacin Gwamnati Saboda Zagin Gwamna Dankwambo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.