Za a halatta kananan matatun mai a Naija Delta

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta halatta kananan matatun mai a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur, tare sayar musu da danyen mai a farashi mai rahusa a karshen shekarar nan.

Matakin na nufin kawo karshen satar danyen man da ake yi daga bututan mai a yankin, wanda ke da haramtattun matatun mai da dama da suke sarrafa man da ake sacewa.

Mazauna yankin na kukan ba sa cin gajiya daga albarkatun man fetur din a yankin nasu.

An bayyana shirin ne bayan wata ganawa da tsakanin mukaddashin shugaba Najeriyar Farfesa Yemi Osinbajo da shugabannin yankin.

Ofishin shugaban kasar ya kuma ce zai tattauna da kamfanonin hakar man masu hedikwata yankin na Naija Delta.

Ko wacce jiha da ke yankin Naijka Delta za ta samu kananan matatun mai biyu da za su fara aiki a watanni uku na karshen wannan shekarar.

Shugabannin yankin sun ce sun yi farin ciki da wannan mataki da gwamnati ta dauka.

Tun a shekarar da ta gabata gwamnati ke ta ganawa da shugabannin al’ummomin yankin Naija Deltadon kawo karshen hare-haren da ake kai wa kan manyan bututan mai mallamar gwamnati da kamfanonin mai.

Sai dai masu tayar da kayar baya na yankin sun ci gaba da barnar da abin da ya jawowa Najeriya asarar miliyoyin daloli, kuma masana tattalin arziki suka ce hakan ya taimaka wajen durkushewar da tattalin arzikin kasar a bara.

Asalin Labari:

BBC Hausa

743total visits,1visits today


Karanta:  Boko Haram Ta Fitar Da Bidiyon Ma’aikatan Jami’ar Maiduguri Da Ta Yi Garkuwa Da Su

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.