Za a Rataye Sojan Nigeria Kan Kisan Abokiyar Aikinsa

Kotun rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yanke wa wani jami'inta hukunci kisa ta hanyar ratayewa, sakamakon kashe wata abokiyar aikinsa da ya yi.

ACM Bernard Kalu ya harbe abokiyar aikinsa ACW Sholape Oladipupo a watan Maris a sansanin sojin sama da ke birnin Makurdi a jihar Benue.

Da yake yanke hukunci kan shari’ar a ranar Talata, alkalin kotun Group Captain Elisha Bindul, ya samu ACM Kalu da laifukan da suka hada da kisan kai, da fasa gida, da yin sojan gona, da kin yin aikinsa na soja, da batar da kayan aiki da kuma bijirewa umarni.

Sai dai hukuncin ba zai tabbata ba sai rundunar sojin sama ta tabbatar da shi.

Haka kuma, lauyan ACM Kalu ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan hukunci, yana mai cewa idan rundunar sojin saman ba ta sauya hukuncin ba, to zai daukaka kara zuwa kotun koli.

Hukuncin na ranar Talata dai ya kawo karshen tsawon lokacin da aka shafe ana yin shari’ar da ta shafi jami’an rundunar sojin saman biyu.

Dama dai tun da fari rundunar sojin saman ta yi alkawarin tabbatar da adalci a yin shari’ar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

763total visits,1visits today


Karanta:  Hukumar EFCC Ta Bankado Miliyoyin Kudi Da Dillalan Mai Su Ka Ci

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.