Za a sa wasan kwallon kafa na kwamfuta a Olympics

Mai yuwuwa a sanya wasan bidiyo na kwamfuta na kwallon kafa a wasannin Olympics a shekarar 2024, inda kwamitin neman karbar bakuncin gasar na Paris yake son tattauna batun tare da kwamitin gasar Olympics na duniya.

Gasar wasan na bidiyo, da ake kira Esports, wadda aka yi a 2016 ta samar da fam miliyan 400, sannan tana da ‘yan kallo a duniya kusan miliyan 320, kuma za a sa ta a cikin wasannin gasar Asia ta 2022.

Shugaban hadin guiwa na kwamitin da ke yi wa birnin Paris zawarcin damar karbar bakuncin gasar ta Olympics Tony Estanguet, ya ce, dole ne mu duba bukatar hakan, ba za mu ce kawai, ba wasan Olympics ba ne.

Jami’in ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na AP, cewa matasa suna da sha’awa a kai, saboda haka za su gana da su, domin fahimtar yadda wasan yake sosai da kuma yadda ya samu karbuwa.

A watan Satumba ne yayin babban taron hukumar wasannin Olympics ta duniya a babban birnin kasar Peru, Lima, inda a hukumance za a tabbatar da ba wa Paris damar karbar bakuncin gasar 2024, da kuma ta 2028 ga birnin Los Angeles

A shekara ta 2019 ne za a fara tsara yadda gasar ta Olympics ta 2024 za ta kasance, sannan bayan gasar 2020 a Tokyo, za a san wasannin da za a kara a gasar Paris.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1048total visits,1visits today


Karanta:  Messi, Ronaldo na cikin fitattun 'yan wasa na duniya na 2017

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.