Za’a kalli kalaman batanci a matsayin ta’addanci – Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa za’a kalli duk wani kalami na batanci a matsayin ta’addanci matukar an samu mutum da laifin aikata hakan.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin taro na malajisar tattalin arziki na kasa akan harkar tsaro a Abuja wanda ya samu halartar gwamnoni, ministoci da sauran masu ruwa da tsaki a dakin taro na fadar shugaban kasa.

A cewar sa, irin wadan nan kalamai za’a dangantasu a karkashin dokar ta’addanci.

Ya kara da cewa cin zarafi da tsorataswa ga al’umma zai zama tamkar ta’addanci, wanda ya bayyana cewar wannan gwamnatin zata dauka da muhimmanci.

Farfesa Yemi Osinbajo yayi kira ga bangarorin addini, yan kasuwa da kuma shuwagabanni ba tare da la’akari da jam’iyya ko bangaren addini ba da su tabbatar sun kyamaci dukkan wasu kalamai na batanci a kowanne irin yanayi.

395total visits,1visits today


Karanta:  Dogara Ya Zama Mamba na Dundundun a Kungiyar Lawyoyi ta Afirka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.