Zaben Anambra: ‘Yaran Nnamdi Kanu za su gane kurensu’

Rundunar ‘yansandan Nigeria ta ce ta daura damarar yin maganin duk wani gungun mutane da za su nemi kawo rudani ko hana gudanar zaben gwamnan da za a yi a jihar Anambra ta shiyyar kudu-maso-gabashin kasar.

‘Yansandan na mayar da martani ne ga barazanar da kungiyar ‘yan aware ta IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ke ci gaba da yi ta hana yin zaben idan gwamnati ba ta amince aka yi kuri’ar raba-gardama kan ballewar yankinsu daga Nigeria ba.

“Ba wanda ya isa ya hana wannan zaben kuma mun dauki matakin cewa duk wanda ya yi kokarin hana wannan zabe za mu kama shi.” In ji Kwamishinan ‘yansanda na jihar Garba Baba Umar cikin wata hira da BBC.

Ya kara da cewa: “Mun gaya wa jama’a cewar babu wani mahaluki ko wata kungiya ko mutum da zai hana wannan zabe; kuma za mu tabbatar mun bayar da cikakken tsaro.”

Wannan gargadin na ‘yansanda dai na zuwa bayan da kungiyar ta IPOB ta kara jaddada aniyarta ta wargaza shirin zaben wanda za a yi a watan Nuwamba.

Wani wakilin BBC a yankin ya ce ko a ranar Lahadi wasu matasa sun yi sowa suna kirari cewa idan babu kuri’ar ta raba-gardama to babu batun yin zabe a jihar ta Anambra, lokacin da gwamnan jihar ya kai ziyara a wani coci.

Asalin Labari:

BBC Hausa

4275total visits,1visits today


Karanta:  Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.