Zaben Kenya: Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya sha gaban Odinga

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya shiga gaba a yawan kuri’u a zaben kasar da aka yi ranar Talata.

Alkalumman da hukumar zaben kasar ta fitar sun nuna cewa kawo yanzu an kidaya kashi 3/4 na yawan kuri’un da aka jefa kuma Shugaba Kenyatta ya samu kashi 55% daga cikinsu; yayin da babban abokin hammayarsa, Raila Odinga, ya samu kashi 44%.

Sai dai tuni da kawance ‘yan hammaya ya yi fatali da sakamakon zaben, yana mai cewa turawan zaben ba su nuna takadun sakamakon zaben da za su tabbatar sahihanci sakamakon da suka bayar ba.

”Wadannan alkalumman na shaci-fadi ne, na bogi ne,” in ji jagoran kawancen adawar Raila Odinga.

Hukumar zaben kasar da ta yi kira ga ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu su jira cikakkaken sakamakon zaben cikin tsanaki.

Mutane a ciki da wajen kasar dai na fargabar sake barkewar rikicin bayan zabe a kasar irin wanda aka yi a shekara ta 2007 lokacin da aka kashe mutane 1’100 wasu kuma 600,000 suka bar muhallansu a kasar ta Kenya.

An dai gudanar zaben cikin kwanciyar hankali a yawancin wurare inda aka ci gaba da zaben a wasu rumfunan har bayan lokacin rufe jefa kuri’a wato karfe 5:00 na yamma agogon kasar.

Kafin dai wani dan takara ya lashe zaben shugaban kasar yana bukatar ya samu sama da kashi 50% na yawan kuri’un da kuma kashi 25% na yawan kuriun da aka jefa a larduna 24 daga cikin 47 da kasar ta Kenya ke da su.

Idan ba wanda ya samu wannan to za a je zageye na biyu na zaben tsakanin ‘yan takara biyu da ke kan gaba.

Karanta:  An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter
Asalin Labari:

BBC Hausa

380total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.