Zaben Kenya: Uhuru Kenyatta ya kayar da Raila Odinga

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Talata data gabata a kasar, a cewar hukumar zabe ta kasar.

Mista Kenyata, wanda shine shugaba mai ci a yanzu sakamakon nasarar da ya samu a shekara ta 2003, ya samu kaso 54.3 na cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, inda abokin adawar sa wato Raila Odinga ya samu kaso 44.7 na cikin dari.

Mista Kenyata ya nemi da a hada kai a kasar bayan sanar da sakamakon zaben, yana mai shaidawa abokan hamayyar sa: “Ina mai kira a gare ku, gaba dayan mu ‘yan kasa guda ne”.

Sai dai a wani bangaren tuni abokan hamayyar ta sa suka nuna kin amincewar su da sakamakon zaben tun kafin a bayyana shi.

Sai dai a wani ci gaban kuma kungiyoyin saka ido na kashashen waje sun amince da sakamakon, inda Mista Kenyata ya bayyana cewar an gudanar da zabe cikin tsafta gami da aiwatar da tsabtataccen zabe ba tare da magudi ba.

450total visits,1visits today


Karanta:  Kenyatta Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.