Zaben Liberia: Brumskine zai sake daukaka kara

Dan takarar shugabancin Liberia karkashin Jam’iyyar Liberty, Charles Brumskine ya bayyana shirinsa na sake komawa Kotun Kolin kasar bayan Hukumar Zabe ta kammala bincikenta, in da ta yi watsi da korafinsa na tafka magudi a zagayen farko na zaben.

Kotun Kolin Liberia ce dai ta bukaci hukumar zaben kasar da ta gudanar da bincike kan korafin Charles Brumskine na Jam’iyyar Liberty da ya ce, an tafka magudi a zagayen farko.

Sai dai a sakamakon da ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, hukumar zaben ta yi watsi da zarginsa, yayin da Brumskine din ya ce, lallai zai sake garzayawa kotun

‘Ba mu da kwarin gwiwa a kan hukumar zaben, wani abin damuwa a game da wannan lamari shi ne yadda aka bai wa hukumar zaben wuka da nama, ta yi zaman sauraren shari’a, sannan kuma ta yanke hukunci, don haka mun sa ran rashin nasara a gabanta amma ba kotun koli ba, in da za mu iya daukaka kara.’

To bisa dukkan alamu, hukumar zaben na da burin gaggauta shiga zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar duk da korafin da Brumskine ke shirin sake shigar wa a kotun kolin.

Henry Flomo Daraktan sadarwa a hukumar Zaben ya ce ba su kaucewa ka’idar aiki da doka ba.

‘Ko a shekarun 2005 da 2011, wannan hukumar zabe, ba ta dakatar da shirinta na ci gaba da zaben ba duk da cewa, akwai batutuwa na zarge-zarge a kasa, an shiga zagaye na biyu duk da shari’ar da ke kasa kamar yadda doka ta ce.’

George Waeh na CDC da Joseph Boakai ne ake saran fafatawarsu a zagaye na biyu.

1516total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.