Zaben Malaysia: Dan shekara 92 ya kada tsohuwar jam’iyyarsa

Mahathir Mohamad

Tsohon firai ministan Malaysia, Mahathir Mohamad mai shekaru 92 ya bada mamaki bayan ya kayar da jam’iyyar da ta mulki kasar na tsawon shekara 60 a zaben shugabancin kasar.

Hukumar zaben kasar ta ce hadakar jam’iyyun siyasa na Mista Mahathir sun lashe kujeru 115, wanda ya zarce 112 da suke bukata domin kafa gwamnati.

Mista Mahathir mai shekara 92 ya kada jam’iyya mai mulki ta Barisan Nasional wadda ta shafe fiye da shekara 60 tana kan mulki.

Ya dade da yin ritaya, amma saboda zaben ya dawo domin karawa da tsohon yaronsa a siyasa, Najib Razak.

“Ba mun zo ramuwa ba ne, so muke mu dawo da doka da oda,” inji Mista Mahathir.

He said he hoped a swearing-in ceremony would be held on Thursday. Mr Mahathir will become the oldest elected leader in the world.

Ya kuma ce yana fatan za a gudanar da bikin rantsar da shi ranar Alhamis, wanda zai mayar da shi shugaban kasa mafi yawan shekaru a duniya.

Saboda wannan nasarar, an bayyana ranakun Alhamis da Jumma’a a matsayin hutu a fadin kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1558total visits,1visits today


Karanta:  Gurbataccen Kwai ya fara isa Asiya daga Turai

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.