Zan koma Nigeria bayan samun yardar likitocina – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya shafe fiye da wata uku yana jinya a Landan, ya ce yana samun sauki kuma zai koma gida ne kawai idan ya samu amincewar likitocinsa, in ji kakakinsa Malam Garba Shehu.

A ranar Asabar ne shugaban ya gana wasu hadimansa a gidan da yake jinya a birnin Landan.

Cikin wadanda suka gana da shugaban har da Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed da Malam Garba Shehu da Mista Femi Adesina da sauransu.

Garba Shehu ya ce: “Buhari ya murmure kuma yana samun kyakykyawar ci gaba.”

Ga cikakkiyar tattaunawar kakakin shugaban da BBC, sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”

5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”

28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba

3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a Landan

23 ga watan Yuli – Ya gana da wasu gwamnoni

26 ga watan Yuli – Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni

431total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.