Zargin luwadi ya hana a ba ni aure — Zango

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Adam Zango ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na neman maza.

Hakan ne ya sa jarumin daukar Al’kur’ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji ba da lalata.

“Wannan abun yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka.” In ji Zango.

Ga dai abin da ya shaida wa Usman Minjibir na BBC Hausa:

Wasu dai musamman masoya na zargin Adam Zango da girman kai.

To amma jarumin ya ce “idan kana maganar masoya kana maganar miliyoyin mutane to ta ya ya zan gamsar da su?

Zango ya nemi masoyan nasa da su rinka yi masa uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa.

Ya kuma nanata maganar da ake alakanta wa ga masu wasan fina-finan Hausa cewa “kudi suke nema”, a inda ya ce “muna yin fina-finan da za su kawo mana kudi.”

Asalin Labari:

BBC Hausa

1150total visits,1visits today


Karanta:  Taylor Swift tayi nasara a shari'ar ta da David Mueller

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.