Zinedine Zidane zai tsawaita zamansa a Madrid

Zinedine Zidane ya tabbatar da cewar zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horas da Real Madrid nan bada dadewa ba.

Zidane ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Asabar kan karawar da Real Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan farko na Spanish Super Cup a ranar Lahadi.

Jaridar Madrid ta AS ta ce za a bai wa kocin dan kasara Faransa yarjejeniyar jan ragamar Madrid zuwa shekara uku.

Zidane ya ci wa Real Madrid kofi shida a wata 20 da ya karbi jan ragamar kungiyar, ciki har da na Zakarun Turai biyu da La Liga da na Zakarun nahiyoyin duniya da UEFA Super Cup.

Kocin ya ce zamansa zai ta’allaka ne da ci gaba da samun nasarori a lokacin da yake jan ragamar Madrid.

”Za ka iya tsawaita zamanka zuwa shekara 10 ko 20, amma nasan inda nake da kuma abin da ya kamata na yi”

Asalin Labari:

BBC Hausa

774total visits,1visits today


Karanta:  Messi, Ronaldo na cikin fitattun 'yan wasa na duniya na 2017

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.